Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya buƙaci ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da kada ya ba shi wani fili a kyauta ko da ya nemi hakan.
Tinubu ya faɗi hakan ne a taron kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) na shekara-shekara a Abuja.
A maimakon haka, shugaban ya ja hankalin Wike da ya bayar da fifiko wajen kammala aikin hanyoyin cikin birnin Abuja domin ci gaban mazaunan birnin.
Yayin da yake gabatar da jawabin, Tinubu ya bayyana ministan babban birnin tarayya Abuja, a matsayin “mai gidan Abuja”.
Tinubu ya ce. manufarsa ba wai ya samu filaye kyauta ba ne, amma ya tabbatar da an samar da jirgin ƙasa wanda zai riƙa jigilar al’umma a birnin.
Wike dai ya riƙa haifar da muhawara tun bayan zama minista sakamakon alwashin da ya ci na rusa gine-ginen da aka yi ba bisa ƙa’ida ba.
Ministan, yayin ziyarar gani da ido a ranar Laraba, ya ce ya kamata a kammala aikin layin jiragen kasa na Abuja (ARMT) nan da watanni takwas.


