fidelitybank

Tinubu ya gana da Ramaphosa a Amurka

Date:

Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya tattauna da takwaransa na Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, inda ya yi maraba da masana’antun hakar ma’adinai na kasar da su zuba jari a fannin bunkasa ma’adanai na Najeriya.

An gudanar da tattaunawar ce a ranar Litinin a birnin New York, gabanin babban taron Majalisar Dinkin Duniya.

A cewar wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya fitar, Tinubu ya ci gaba da yunkurinsa na bunkasa tattalin arziki na diflomasiyya don jawo hankalin masu zuba jari a yayin ganawar.

“Kamfanonin hakar ma’adinai na Afirka ta Kudu suna da rawar da za su taka a fannin bunkasa ma’adanai a Najeriya,” in ji shugaban Najeriyar.

“Yan kasuwar ku sun kyautata sosai a harkar sadarwa ta Najeriya.”

“Muna da arzikin ma’adinai mai yawa a fadin kasarmu, kuma kuna da kwarewa sosai a wannan fannin.”

“Saboda haka, muna sa ran samar da ayyukan yi da kuma sakamako mai amfani a wannan fanni a matsayinmu na ‘yan’uwan juna.”

Tinubu ya kuma bukaci Afirka ta Kudu da ta haɗa kai da Najeriya wajen yin kira ga yin garambawul ga cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya domin taimaka wa Afirka wajen yaƙar talauci da tabarbarewar tattalin arziki

legit.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp