fidelitybank

Tinubu ya gana da Macron a Faransa

Date:

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawa da shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron a ranar farko ta ziyarar aiki da shugaban na Najeriya ke yi a ƙasar.

A yau Alhamis, Tinubu ya isa fadar shugaban Faransa ta Elysee tare da tawagarsa, wadda ta hada da ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar da ministan kuɗi, Wale Edun da na tsaro Badaru Abubakar.

A ɓangare ɗaya shugaban Faransa ya shiga ɗakin taron ne tare da ƙaramin ministan harkokin waje na ƙasar, Thani Mohamed Soilihi da kuma ministan tsaro na Faransa, Sebastien Lecornu da sauran jami’ai.

Ana sa ran Najeriya da Faransa za su ƙulla hulɗoɗi na diflomasiyya da kasuwanci a lokacin ziyarar ta shugaba Tinubu, wadda take zuwa bayan ragin tagomashi da Faransa take samu a Afirka.

Dangantaka ta yi tsami tsakanin Faransa da ƙasashen da ta rena a yammacin Afirka, kamar Nijar da Burkin Faso da Mali.

Ƙasashen sun yanke huldar diflomasiyya da Yamma tare da karkata akalarsu zuwa ɓangaren Rasha.

A matsayinsa na shugaban ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka, Tinubu ya yi ƙoƙarin ganin ƙasashen Nijar da Mali da Bukina Faso sun koma tafarkin dimokuraɗiyya sai dai har yanzu abin ya ci tura.

legit news 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp