Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yaba wa Firaiministan India Nerandra Modi game da karɓar baƙunci taron G20 ya kuma nuna jin daɗinsa game da gayyatarsa da ya yi.
“A matsayina na shugaban ƙasar da tafi shahara tsakanin kasashen baƙaƙen fata, ni ma zan bi sawun sauran shugabannin ƙasashen duniya wajen tabbatar goben ƙasar mu Najeriya ta zama mai haske – tare da duka sauran ƙasashen nahiyar Afrika,” in ji Tinubu.
“Kuma a shirye nake wajen mun sake ƙarfafa tsare-tsarenmu kan dimokraɗiyya da ci gaba da yan ƙasarmu mzaune waje da kuma yawan al’umarmu.”


