Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyeson Wike, ya ce gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta karɓi Najeriya ne lokacin da tattalin arzikin ƙasar ya kusa durkushewa.
Wike ya bayyana haka ne a cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels ranar Juma’a.
Ya yi watsi da iƙirarin cewa gwamnatin Tinubu ta lalata ɓangaren tattalin arzikin Najeriya.
“Ya gaji tattalin arzikin da ya samu tawaya, wanda kuma ya kusa durkushewa,” in ji Wike.
Ministan na Abuja ya ce Allah ne ya ceci Najeriya da ya kawo shugaba Tinubu saboda kaɗan ya rage a binne ƙasar.
“Najeriya ta yi sa’a da zuwan Tinubu saboda ƙiris ya rage a binne ta. Mun yi farin ciki Tinubu ya zo ya ce hakan ba zai faru ba, ‘Ba zan ba ri ku shiga matsala ba”.
Ya ce cire tallafin man fetur da aka yi yana da alfanu sosai saboda zai samar wa jihohi ƙarin kuɗaɗen kashewa, ba kamar yadda wasu ke cewa tsarin ba mai kyau bane duk da cewa an fuskanci matsaloli.
Wike ya ce ya yi wuri a yi wa gwamnatin Tinubu alkalanci a ƙasa da shekara biyu kan mulki, inda ya yi kira da a ci gaba da marawa gwamnatin baya.