Dan takarar shugaban kasa na jamâiyyar All Progressives Congress, Asiwaju Bola Tinubu, ya fara tattaunawa da malaman addini a kan cece-kucen da ya biyo bayan tikitin takarar musulmi da musulmi.
Kakakin kungiyar kamfen din Tinubu (TCO), Bayo Onanuga ne ya bayyana haka a wata hira da jaridar The Punch ranar Talata.
Onanuga ya bayyana cewa tsohon gwamnan Legas ya fara tattaunawa da manyan malaman addini da sauran masu ruwa da tsaki domin bayyana zabin Shettima a matsayin mataimakinsa.
Ya ce, sansanin Tinubu ya yanke shawarar kada a bayyana ci gaban da aka samu a bainar jamaâa har sai an kammala wasu batutuwa, inda ya ce akwai tsarin da ba za a bayyana shi ba.
Onanuga, ya bayyana cewa, shugaban nasa zai yi jawabi ga manema labarai idan an kammala shawarwarin.
Ya ce: âBa mu yin talla a kafafen yada labarai. Muna magana da mutanen da abin ya shafa. Tuni dai aka fara aikin tuntubar. Ba mu yin surutu da yawa game da shi don ba a buga shi ba.