Bayan gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, wanda Bola Ahmed Tinubu na jam’iyar APC ya yi nasarar zama shugaban kasa, yanzu kuma hankali ya koma kan irin ƙalubalen da ke gaban sabon zaɓaɓɓen shugaban mai jiran gado.
Masana sun fara bayyana wasu jerin ƙalubala da ke kan gaban Tinubu, tare da kira gare shi da kada ya kalli ɓangaranci wajen yi wa kasa aiki.
BBC ta tattauna da Farfesa Tukur Abdulkadir, wani massanin kimiyar siyasa da ke jami’ar jihar Kaduna wanda ya ce, akwai buƙatar Tinubu ya fara aiki cikin gaggawa ba tare da ɓata lokaci ba.
“Ya kalli abubuwan da suka faru a 2015, kada ya sake ya maimaita abubuwan da Buhari ya yi a baya, kamar jinkiri wajen naɗa ministoci da shugabannin hukumomin gwanati.
“Kada ya kalli ɓangaranci a shugabancinsa domin kuwa Najeriya zai shugabanta ba wani ɓangare ba,” in Farfesa Tukur.