Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dawo gida daga bulaguron da ya yi zuwa Turai, kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa ta bayyana.
Mai bai wa Tinubu shawara kan yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, wanda ya yi sanarwar a shafinsa na X, ya yi wa Tinubu maraba da komawa gida.
Ya wallafa “maraba da shugaban ƙasa!,” kamar yadda ya rubuta.
Shugaba Tinubu ya yi tafiya zuwa Netherlands inda ya gana da Firaiministan ƙasar Mark Rutte, mako biyu da suka gabata, daga nan kuma ya je Saudiyya domin halartar taron taron tattalin arziki na duniya.
Daga nan kuma ya yi bulaguro zuwa Turai bayan taron na WEF.
A ranar 22 ga watan Afrilu ne shugaba Tinubu ya kai ziyarar aiki zuwa Netherlands.
An yi tunanin shugaban zai koma Najeriya bayan taron da ya halarta a Saudiyya sai dai bai koma ba, lamarin da ya janyo cece-kuce game da inda shugaban yake.