A karshe dai shugaba Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan wata ziyarar sirri da ya kai kasar Faransa na tsawon makonni biyu.
Jirgin shugaban kasar ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja a daren ranar Talata.
Tinubu ya samu tarba ne daga shugaban ma’aikatan sa, Femi Gbajabiamila, mai baiwa kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, sakataren gwamnatin tarayya, George Akume da kuma ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike.
Jam’iyyun adawa sun caccaki shugaban kasar kan zargin yin watsi da kasar a cikin matsalolin tsaro da tattalin arziki da suka addabi al’ummar kasar.
Wasu daga cikin jiga-jigan ‘yan adawa na ganin cewa shugaban bai da wani dalili na yin wata ziyarar sirri a lokacin da kasar ke zubar da jini.