Shugaba Bola Tinubu, ya nada tsohon karamin ministan kwadago Festus Keyamo a matsayin minista.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin wani zama da aka yi.
Tinubu ya kuma maye gurbin Maryam Shetty, wacce ya nada a matsayin minista a ma’aikatar mata, da Dr Maigari Mahmud daga jihar Kano.