fidelitybank

Tinubu ya cire malaman jami’o’i da na kwaleji daga tsarin biyan kudi na IPPIS

Date:

Majalisar zartarwa ta kasa ta cire malaman jami’a, da na kwalejojin ilimi da fasaha daga tsarin albashi na Integrated Personnel Payroll Information System (IPPIS).

Ministan Ilimi Farfesa Tahir Mamman ya ce Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ne ya ba da umarnin yin hakan a zaman majalisar da ya jagoranta a yau Laraba.

Ya ƙara da cewa hakan zai bai wa shugabannin cibiyoyin ilimin damar ɗaukar ma’aikata ba tare da sun nemi amincewar ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya ba.

“A taƙaice, shugaban ƙasa da majalisar sun nuna damuwarsu ne kan yadda ake gudanar da jami’o’in, amma hakan ba shi da alaƙa da zaɓar wani tsarin biyan albashi ko kuma zargin rashin adalci,” a cewar ministan kamar yadda kafofin yaɗa labaran Najeriya suka ruwaito shi yana faɗa jim kaɗan bayan kammala zaman a fadar shugaban ƙasa.

Ƙungiyar malaman jami’a ta ASUU ta daɗe tana neman gwamnatin Najeriya ta cire su daga tsarin, wanda ya hana su gudanar da wasu ayyuka da kuma ƙayyade kuɗin da za su samu a matsayin albashi.

Hakan na nufin yanzu jami’o’in da sauran kwalejoji za su dinga biyan malamansu albashi da kansu ba sai sun dogara da gwamnatin tarayya ba, in ji Ministan Yaɗa Labarai Muhammed Idris.

latest news nnn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp