A ranar Alhamis din da ta gabata ne shugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci majalisar dattijai da ta tabbatar da sabbin ministoci bakwai.
Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika daga bangaren zartarwa kuma shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya karanta a benen babban zauren majalisar.
A ranar Larabar da ta gabata ne shugaba Tinubu ya kori akalla ministoci biyar tare da soke wasu ma’aikatu biyu.
Shugaban ya kuma nada sabbin mukamai ga wasu Ministoci a zaman majalisar ministocin na ranar Laraba.