Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Ahmed Bola Tinubu, yanzu haka yana jihar Kano domin bude ofisoshin yakin neman zabensa.
Tinubu wanda al’ummar jihohin Kano, Jigawa da Zamfara suka yi masa tarba a ranar Asabar, ya samu tarba daga dubban magoya bayansa a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano.
Gwamnonin jihohin Kano, Jigawa da Zamfara, Abdullahi Umar Ganduje, Alhaji Badaru Abubakar da Alhaji Mohammed Bello Matawalle, sun tarbi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, wadanda suka yi tururuwa a jihar tare da daruruwan magoya bayansu.
A cikin shirin ziyarar, Tinubu zai kuma kai ziyarar ban girma ga Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero tare da ganawa da sarakunan Gaya, Rano, Bichi da Karaye.
Dan takarar jam’iyyar APC zai gudanar da taron tattaunawa da ‘yan kungiyar Tijjaniyya, Kadriyya, Ahlus Sunna, shugabannin kungiyar CAN, kungiyoyin goyon bayan APC na jihar da sauran ayyuka.