Gwamnatin tarayya ta amince da sake bude iyakokar Seme domin shigo da motoci.
Daraktan Sufurin Jiragen Sama na Ma’aikatar Sufuri, Ibrahim Musa ne ya bayyana hakan a ranar Laraba.
Musa, wanda ya yi jawabi a taron kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, ECOWAS, da aka shirya tsakanin jami’an Najeriya da jamhuriyar Benin, ya bayyana cewa ci gaban ya biyo bayan korafe-korafen da masu jigilar kaya da ke aiki a kan iyakar Seme.
Ya ce: “Na kasance a nan tare da tsohon Ministan Sufuri lokacin da masu jigilar kayayyaki suka roki cewa a sake kunna kan iyakar don zirga-zirgar kayayyaki da ayyuka kyauta.
“Tsohuwar ministar ta sa mu shirya takarda kan hakan. An yi la’akari da shi kuma an aika zuwa ga gwamnati.”
Hakazalika, shugaban hukumar kwastam na yankin Seme, Dera Nnadi, wanda shi ma ya yi magana a wajen taron, ya koka kan yadda hukumar ta lura da raguwar kudaden shigarta tun bayan da gwamnatin da ta shude ta dakatar da shigo da motoci ta kan iyakokin kasa.
Nnadi ya ce: “Tsohon Ministan Sufuri, da yake amsa wasu bukatunmu da masu ruwa da tsaki, ya yi alkawarin kai su Majalisar Zartaswa ta Tarayya, FEC, daya daga cikinsu shi ne yadda za a bude iyakar.
“Ma’aikatar ta sanar da mu cewa an rubuta takardar zuwa FEC kuma an karbe ta kuma za a ba da ita ga sabuwar gwamnati, ya ba mu tabbacin cewa an amince da duk bukatun.”


