Hukumar kula da Da’ar Ma’aikata ta Najeriya ta ce dole ne zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da gwamnonin ƙasar 28 da ke jiran rantsuwa su bayyana kadarorinsu kafin ranar 29 ga watan Mayu.
Haka kuma hukumar ta ce su ma zaɓaɓɓun ‘yan majalisun wakilai da na dattawa za su bayyana nasu kadarorin kafin ranar 5 ga watan Yuni lokacin da za a rantsar da su.
Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito mai magana da yawun hukumar Mrs Veronica Kato, na cewa bayyana kadarorin, wani ɓangare ne na shirye-shiryen shan ratsuwar kama aiki ga zaɓaɓɓun shugabannin kamar yadda dokar ƙasar ta tanadar.
Mrs Kato, ta ce da yawa daga cikin zaɓaɓɓun sun fara karɓar fom ɗin bayyana kadarorin a rassan ofisoshin hukumar da ke faɗin jihohin ƙasar, kuma ana sa ran za su mayar da fom ɗin zuwa ofisoshin tare da bayyana kadarorin kafin ranar rantsar da su.
Kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi cewa masu riƙe da muƙaman siyasa su bayyana kadarorin da suka mallaka a lokacin da za su kama aiki da kuma a lokacin da suka kammala wa’adin mulkinsu.