Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan harin bam da sojojin Najeriya suka kai a Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna a ranar Lahadin da ta gabata, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya fitar ranar Talata, shugaban ya jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa da kuma gwamnatin jihar Kaduna.
“Shugaba Bola Tinubu ya jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa, da jama’ar jihar da kuma gwamnatin jihar Kaduna kan tashin bam a wani kauye da ke Tundun Biri a karamar hukumar Igabi a jihar.
“Shugaba Tinubu ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, mai tayar da hankali, kuma mai raɗaɗi, yana mai nuna fushi da baƙin ciki game da mummunar asarar rayukan da aka yi a Najeriya.
“Shugaban kasa ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da yin kira da a kwantar da hankula yayin da hukumomi suka yi nazari sosai kan lamarin.
Sanarwar ta kara da cewa “Shugaban ya kuma ba da umarnin kulawar gaggawa ga wadanda abin ya shafa yayin da yake addu’ar samun lafiya ga rayukan wadanda suka mutu.”
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya tabbatar da cewa rundunar Sojin ta dauki alhakin kai harin ta sama wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a ranar Lahadi.


