Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin a gaggauta sayo kayan aikin da za a bi domin dakile karuwar satar mutane da rashin tsaro.
Wike ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a wani taron manema labarai a Abuja.
A cewarsa, babu wuraren da ake bibiyar masu aikata laifuka a FCTA sai dai a hedikwatar ‘yan sanda da ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.
Ya ce: “Ba a samar da kayan aiki da yawa ba. Motocin hukumomin tsaro ba su nan. Ba za ku iya yarda cewa kayan aiki don bin diddigin masu laifi ba su nan. Idan wani abu ya faru sai su koma ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ko hedikwatar rundunar. Ba haka ya kamata ya kasance ba.
“Haka kuma, kafin mu hau, ‘yan sanda sun ce sun bukaci a sayo wasu adadin babura inda motocin ba za su iya zuwa wurare masu nisa da tsaunuka ba. Abin takaici, ba a samar da su ba, amma za mu yi hakan a yanzu.
“Tsaro ba wannan kayan aikin bane kawai. Hakanan dole ne ku kwadaitar da ma’aikata. Ba na son tattauna dabarun saboda muna tattaunawa kan tsaro a yanzu. ”
Wannan ci gaban ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da matsalar rashin tsaro a babban birnin kasar.
Majalisar Dattawa ta gayyaci Wike game da karuwar rashin tsaro.
A halin da ake ciki kuma, kokarin da hukumomin tsaro suka yi ya kai ga ceto mazauna Abuja da aka yi garkuwa da su.