Jigo a jam’iyyar APC ta kasa, Sanata Bola Tinubu, ya bayar da gudummawar Naira miliyan 75 ga wadanda harin da ‘yan bindiga suka kai cocin St. Francis Catholic Church, a ranar Lahadin da ta gabata.
Tinubu, mai neman tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, ya bayar da tallafin ne a ranar Litinin a Owo, a ziyarar da ya kai, domin jajantawa Gwamna Rotimi Akeredolu da al’ummar garin.
Akeredolu, wanda ya sanar da bayar da tallafin a fadar Olowo na Owo, Oba Ajibade Ogunoye, ya godewa shugaban jam’iyyar APC bisa wannan karimcin.