Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada kakakin kungiyar dattawan Arewa (NEF), Dr Hakeem Baba-Ahmed a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin siyasa a ofishin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima.
Dr Baba-Ahmed kani ne ga Datti Baba-Ahmed, abokin takarar Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023.
Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafin sa na X a ranar Litinin.
Ya rubuta: “Lokaci ya yi da zan bayyana wa jama’a cewa na karɓi kiran na zama mai ba da shawara na musamman (Siyasa) ga VP. Wannan ba lokaci ba ne na suka da za ku iya zama masu amfani wajen mayar da ƙasar. Ina da girma da ƙasƙantar da kai. Don Allah a yi mini addu’a da Nijeriya.”


