A ranar Juma’a ne jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya amince da gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, da mataimakinsa, Obafemi Hamzat, a karo na biyu a kan karagar mulkin jihar Legas.
Babban Sakataren Yada Labarai na Sanwo-Olu, Gboyega Akosila, ne ya bayyana hakan a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Tuwita wanda ke dauke da bidiyon Tinubu na daga hannun Gwamnan da Mataimakin sa.
Ku tuna cewa a ranar 29 ga Afrilu, 2022, Sanwo-Olu ya sayi fom din takarar gwamna na jam’iyyar APC na Naira miliyan 50, domin sake tsayawa takara a karo na biyu.