Shugaba Bola Tinubu ya amince da Naira biliyan 683,429,268 a matsayin asusun shiga tsakani na shekarar 2024 ga manyan makarantun gwamnati a kasar nan.
Sakataren zartarwa na Asusun Tallafawa Manyan Makarantu, TETFUnd, Sonny Echono, ne ya bayyana haka a ranar Juma’a a taron tsare-tsare na asusun tare da shugabannin cibiyoyin da suka ci gajiyar tallafin a Abuja.
A cewarsa, daga jimillar kashi 90.75 bisa 100 an ware domin rabawa kai tsaye, kashi 8.94 na wasu ayyuka na musamman da aka kebe yayin da kashi 2.27 cikin 100 aka ware domin magance matsalolin da suka kunno kai.
Ya kuma bayyana cewa kowace jami’ar da za ta ci gajiyar shirin za ta samu, a shekarar 2024, jimillar N1,906,944,930.00, kowace kwalejin fasaha za ta samu N1,165,355,235.00, yayin da kowace Kwalejin Ilimi za ta samu N1,398,426,282.00.
“Ina mai farin cikin sanar da ku cewa, shugaban kasa ya amince da ka’idojin fitar da kudade na shekarar 2024 a jimillar N683,429,268, 402.64. Daga wannan jimillar, an ware kashi 90.75 cikin 100 don rabawa kai tsaye da kuma 8.94% don wasu ayyuka na musamman da aka keɓe. An ba da izinin daidaitawa na 2.27 % don baiwa Asusun damar amsa matsalolin da ke tasowa.
“Wannan ya hada da bambanci tsakanin ainihin tarin da kuma hasashen da aka yi a watan Nuwamba da Disamba na 2023 kamar yadda Mista Shugaban kasa ya nema kuma ya amince,” in ji Echono.
A nasa bangaren, mukaddashin sakataren din-din-din na ma’aikatar ilimi ta tarayya, Zubairu Abdullahi, ya ce akwai wani sabon fata da jajircewa daga shugaban kasa wanda kowa ya kamata ya sanya a gaba.
Ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su kara zage damtse don cimma buri na sabunta burin Tinubu.