fidelitybank

Tinubu ya amince da kafa asusun more rayuwa a jihohi 36

Date:

Shugaban ƙasa Bora Ahemd Tinubu, ya amince da kafa asusun gina ababen more rayuwa a jihohi 36, a wani mataki na rage wa yan kasa radadin cire tarafın man fetur.

Shugaban ya amince da matakin ne a lokacin taron wata wata na kamitin kula da asusun raba kudin, shiga na gwamnatin kasar (FAAC) da aka gudanar ranar Alhamis a Abuja.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Dele Alake ya fitar, ya ce sabon asusun zai taimaka wa jihohin kasar wajen zuba jari a bangarorin sufuri da harkokin noma da gina tituna da kasuwanni da kiwon dabbobi da bangaren lafiya da ilimi musamman a matakin farko, da wutar lantarki da ruwan sha domin habaka tattalin arzki da samar da ayyukan yi ga yan kasar.

Kwamitin ya kuma amince da ajiye wani bangare na kudin da ake rabawa a kowane wata domin takaita tasirin aeruwar shiga da za a iya samu sakamakon matakan cire tallatin mai da daidata farashin dala tare da hauhawar farashin kayayyaki za su iya haifarwa.

Kwamitin ya ce, daga cikin naira tiliyan 1.9 na kudin shigar da aka samu a watan Yunin 2023, naira biliyan 907 ne kawai za a raba tsakanin matakan gwamnatin kasar uku, yayin da za a ajiye naira biyan 790 a asusun.

Wadannan kudaden da za a riƙa ajiyewa za su taimaka wajen samar da asusun gina ababen more rayuwa tare da aiwatar da wasu abubuwa, domin tabbatar da an yi amfani da kudin tallafin wajen gina muhimman abubuwan ci gaba, domin inganta rayuwar yan kasar kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Haka kuma kwamitin ya yaba wa shugaban kasar bisa matakin cire tatafin man tare da bullo da matakai daban-daban na tallafa wa ‘yan kasar domin rage masu raɗadin cire tallafin.

legit new

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp