Gwamnatin Tarayyaa ta amince da rancen dala miliyan 750 daga bankin duniya, domin gina kananan wuraren samar da wutar lantarki 1,200 a yankunan karkara a fadin kasar nan.
Manajan Darakta kuma Babban Jamiāin Hukumar Raya Wutar Lantarki ta Karkara, Abba Aliyu ne ya bayyana hakan, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a taron hadin gwiwar samar da wutar lantarki na yankunan karkara da aka gudanar a Legas.
A cewar Aliyu, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya amince da samar da wutar lantarkin da nufin samar da makamashi ga āyan Najeriya mazauna yankunan karkara.
Ya kuma ce, an amince da rancen ne domin cike gibin da ke tsakanin āyan Najeriya da ke da kamfar wutar lantarki da kuma wadanda ba su da wutar lantarki.
Ya kara da cewa kashi 23 cikin 100 na alāummar kasar nan miliyan 85 da ba su da wutar lantarki, za a ba su wutar lantarki idan an kammala aikin.