fidelitybank

Tinubu ya amince a biya Super Eagles da sauran bashin su na biliyan 12

Date:

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da biyan Naira biliyan 12, domin biyan kudaden da ake kashewa ga Super Eagles da sauran kungiyoyin wasanni na kasa daban-daban.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a shafin X na Cibiyar Yada Labarai ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sanarwar ta ce, biyan kudin zai shafe watanni 15 na albashin manyan kociyan kungiyar, da biyan alawus-alawus da kuma alkawuran da ya kamata a yi wa manyan kungiyoyin kasa da kasa, mata, da kuma ‘yan kasa da shekara 20.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Shugaba @officialABAT ya amince da biyan N12billion na baya bayan nan ga kungiyoyin kwallon kafar Najeriya na wasanni daban-daban da suka hada da Super Eagles da sauransu.

“Biyan ya hada da cire albashin manyan kocin kungiyar na tsawon watanni 15, da biyan alawus-alawus da kuma alkawuran da ya shafi manyan kungiyoyin kasa da mata da kuma ‘yan kasa da shekara 20.

“Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan wasan Super Eagles na Najeriya ke shirin shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika, wanda ake sa ran za a fara a karshen wannan watan.”

nigeria 
news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp