fidelitybank

Tinubu ya aike da sakon ta’aziyya ga iyalan Dantata

Date:

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya aike da saƙon ta’aziyarsa ta rasuwar Alhaji Aminu Ɗantata, attajirin ɗankasuwa da ya rasu a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, wanda ya rasu yana da shekara 94 a duniya.

Tinubu ya bayyana rasuwar hamshaƙin ɗankasuwar, wanda aka binne a ƙasar Saudiyya a matsayin “rashi ga ƙasar baki ɗaya’.

Tinubu ya yaba da gudunmuwar da marigayin ya bayar wajen ciyar da Najeriya gaba, “musamman a ɓangaren ilimi da kiwon lafiya,” kamar yadda sanarwar da mai magana da yawun shugaban, Bayo Onanuga ya fitar.

Tinubu ya ce, “mun yi rashi na babban ɗankasuwa, mai kishin ƙasa, kuma dattijon arziki wanda ya ya taimaka wajen gina ƙasarmu Najeriya.”

Tinubu ya ce za a riƙa tuna Ɗantata a matsayin ɗankasuwa mai sanin ya kamata wanda ya bayar da gudunmuwa wajen haɗin kan ƙasa ta hanyar kasuwancinsa da ayyukan jinƙai, “wanda ya amfanar da ƴan Najeriya da ba za su ƙirgu ba.”

A ƙarshe Tinubu ya jajanta wa iyalan marigayin tare gwamnati da al’ummar Kano baki ɗaya bisa.

besda salary

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...

An gargadi Borno da Yobe da Jigawa su zama cikin shirin ambaliya

Akwai yiwuwar samun ambaliya a jihohin Borno, Jigawa da...

Kano na cikin jihohin da ba su yi katin zabe sosai ba – INEC

Bayanan da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya...

Mun gano filin wasa na Sani Abacha ba shi da inganci – NPFL

Hukumar shirya gasar cin kofin kwararru ta kasa (NPFL),...

Jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna ya ya fadi

Jirgin ƙasa ɗauke da fasinjoji da ya taso daga...

Jami’in mu bai saci naira biliyan 6.5 ba – Gwamnatin Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta karyata rahoton da ya zargi...

Gwamnatin Kano ta gargadi Matasa da ‘yan Gwangwan kan sayen kayan gwamnati

Gwamnatin Jihar Kano ta gargadi matasa da ’yan kasuwa...

NIMET ta gargai Borno kan ambaliya da sauran jihohi

A baya-bayan nan ne hukumar hasashen yanayi ta Najeriya...

An kashe kwamandan Boko Haram a tafkin Chadi

Sojojin Jamhuriyar Nijar sun sanar da kisan wani jagoran...

Hisbah za ta yi wa ‘yan Daban Kano aure

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da wani...
X whatsapp