Shugaba Bola Tinubu ya aike da saƙon alhininsa ga iyalan marasautar Kuwaita da gwamnati da ma al’ummar ƙasar baki ɗaya kan rasuwar sarkin ƙasar Sheikh Nawaf al-Ahmad al-Sabah.
Cikin saƙon jajen da mai magana da yawun Tinubun ya fitar, shugaban ya yaba da nasarorin da marigayin ya samu a zamanin mulkinsa.
Shugaba Tinubu ya kwatanta marigayin da mai son zaman lafiya da tausayi – wanda ya yi wa fursunonin siyasa afuwa – don samun zaman lafiya da ci gaban ƙasarsa.
Yau da safe ne dai aka sanar da rasuwar sarkin Sheikh Nawaf al-Ahmad al-Sabah mai shekara 86 a duniya.
Tuni dai aka sanar da naɗin sabon sarkin ƙasar, mai suna Sheikh Meshal al-Ahmad al-Jaber al-Sabah, wanda ɗan uwa ne ga Sheikh Nawaf.

Sabon sarkin wanda tuni ya fara gudanar da wasu ayyuka, ya shafe akasarin rayuwarsa a ɓangaren tsaro da tattara bayanan sirri na Kuwait.
Tuni aka ayyana makokin kwana 40 a faɗin ƙasar, domin nuna alhini kan rasuwar tsohon sarkin.