Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa, ya kalubalanci shugaban kasa Bola Tinubu da ya yi gaggawar magance korafe-korafen ‘yan Najeriya.
A wani jawabi da ya yi a fadin jihar a yammacin Lahadin da ta gabata, Fintiri ya jaddada cewa bai isa ba shugaban kasa ya fadawa ‘yan Najeriya cewa ya ji kukansu. A cewarsa, bai kamata ‘yan Najeriya su jira har abada ba domin a dauki matakan da suka dace.
Gwamnan wanda ya yi magana a kan zanga-zangar #BadBadGovernance a jihar Adamawa, ya yabawa mazauna jihar bisa yadda suka gudanar da rayuwarsu cikin lumana, duk da cewa ya kamata gwamnatin tarayya ta yi biyayya ga kiran jama’a.
Ya ce, “Kila zanga-zangar ba ta da farin jini musamman saboda yadda aka yi ta a wasu jihohin, amma sakon a bayyane yake kuma bukatun na gaskiya ne. Babu daya daga cikinmu da zai iya musun cewa akwai yunwa da talauci gaba daya”.
Ya kara da cewa a matsayinsu na shugabannin jama’a, wadanda ke cikin gwamnati dole ne, a kowane lokaci, ba wai kawai su saurara ba, har ma su yi aiki.
“Darussan da ya kamata mu dauka daga zanga-zangar shine tunatarwa akai-akai cewa bai isa mu gaya wa ‘yan kasar da muka ji ba. Dole ne a ganmu muna yin abin da ake bukata wajen samar da mafita ga matsalolin ‘yan kasa,” in ji gwamnan.
Bayan gudanar da zanga-zanga a ranakun 1 da 2 ga watan Agusta, musamman ma babban birnin jihar, Yola, zanga-zangar ta kusan kamawa a jihar Adamawa.
Babu wani tashin hankali da aka samu a jihar.