Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya ce Najeriya na cikin wani mawuyacin hali a shekarar 2022, sakamakon fuskantar matsaloli da dama da ke barazana ga haɗin-kai, ɗorewar zaman lafiya da kuma makomarta har sai da shugaba Bola Tinubu ya zo ya cece ta bayan hawa mulki a shekarar 2023.
Ribadu ya bayyana haka ne a wani jawabi a taron kwalejin horas da sojoji ta Najeriya, inda ya bayyana lamarin da mai muni – inda sassan ƙasar duka suka shiga cikin matsalolin rashin tsaro.
Ya ce kafin zuwan Tinubu kan mulki matsaloli sun dabaibaye ƙasar – kama daga ayyukan masu ta da ƙayar-baya a arewa maso gabas sai kuma matsalar ƴanbindiga a arewa maso yamma, ta da zaune tsaye a yankin Neja Delta da kuma masu fafutukar ɓallewa a kudu maso gabashin ƙasar.
Ribadu ya ƙara tabbatar da hoɓɓasar da gwamnatin Tinubu take yi wajen ganin ta magancew matsalolin tsaro da ta gada.
A cewarsa, an ɗauki tsauraran matakai wajen dawo da zaman lafiya a faɗin ƙasar, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Ya ce ƙoƙarin da gwamnati take yi wajen yaƙi da masu ta da ƙayar-baya ya kai kashe sama da ƴan ta’adda 13,500, yayin da sama da mayakan Boko Haram da na ISWAP 124,000 haɗe da iyalansu ne suka miƙa.