Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda, ya ce, Bola Tinubu, zai magance matsalar cin hanci da rashawa yadda ya kamata idan aka zabe shi a matsayin shugaban Najeriya a 2023.
Yuguda ya bayyana hakan a shirin gidan talabijin na Channels, Sunrise Daily a ranar Litinin.
Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama ya yarda cewa, a matsayinsa na tsohon dan jam’iyyar PDP ya ga manyan cin hanci da rashawa a cikin shekaru 16 na mulkin jam’iyyar, wanda gwamnatin yanzu ta gada.
Ya soki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya ce ta gaza cika alkawarin da ta dauka na yaki da cin hanci da rashawa, duk da kokarin da ta yi.
Da yake karin haske, Yuguda, wanda jigo ne a jam’iyyar APC, ya ce yana da yakinin cewa da Tinubu a kan karagar mulki za a magance matsalar cin hanci da rashawa.
“Cin hanci da rashawa matsala ce da ta gada kuma tana kara ta’azzara ko muna so ko ba mu so sai ’yan Najeriya sun gane cewa cin hanci da rashawa ne ke kashe mu kuma za ta kashe mu a karshe. Kowa ya lalace, ina jin tsoro.
“Gwamnatin ba ta gaza ba saboda abin da aka gada ke nan. Ina cikin gwamnatin da ta gabata kuma na ga cin hanci da rashawa.
“Wannan gwamnati ta zo ne da niyyar yaki da cin hanci da rashawa amma ba mu san irin nakiyoyin da aka binne a kan hanyarsu ta nakasa ba.


