Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya bayyana cewa, zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bukace shi da ya janye wa Sanata Godswill Akpabio takarar shugabancin majalisar dattawa karo na 10.
Gwamnan ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai a ranar Litinin da ta gabata a lokacin da ya isa filin jirgin saman Muhammadu Buhari, Onueke a Ebonyi.
Umahi ya bayyana cewa ya tattauna da Tinubu kan takararsa ta neman shugabancin majalisar dattawa kuma ya amince da bukatarsa domin amfanin jam’iyyar APC da shiyyar Kudu maso Gabas.
“Na tattauna batun da zababben shugaban kasar a lokacin da yake birnin Paris kuma ya gayyace ni bayan ya dawo kasar.
“Abin alfahari ne da Tinubu ya gayyace shi kuma ya shaida min cewa ya yi alkawari. Hakkinsa ne a matsayinsa na zababben shugaban kasa ya yi alkawari kuma duk wanda ya tsaya takarar irin wannan mukami ya yi alkawari.
“Saboda haka na yarda saboda ba na son in kasance mai rugujewar ci gabansa.”
Da yake magana kan janyewar sa, ya ce, “Siyasa ita ce tattaunawa, bayarwa da karba, ba za mu iya ci gaba da adawa da komai ba.
“Idan aka yi la’akari da kokarin da muke yi na inganta jam’iyyar All Progressives Congress, APC, shiyyar Kudu-maso-Gabas za ta samu matsayi na gaske,” in ji shi.