Tsohon ɗantakarar shugaban ƙasa a Najeriya, Atiku Abubakar, ya zargi shugaba, Bola Tinubu da yunƙurin tauye haƙƙin ma’aikata, tare da hana su bayyana halin ƙuncin rayuwa da suke ciki.
Atiku ya bayyana cewa janye tallafin man fetur da Tinubu ya yi a ranar rantsar da shi ne ya haifar a matsalar tattalin arziki a ƙasar, wanda a cewarsa ya jefa masu ƙaramin ƙarfi a ƙasar cikin yunwa da rashin tabbas.
Ya ce domin Tinubu ya yi yunƙurin rage raɗaɗin da ƴankasar ke ciki ne ta hanyar ɗaukar alƙawarin ƙara albashi ga ma’aikatan ƙasar, “amma alƙawarin, kamar sauran alƙawura da ya ɗauka, sai da aka yi wata 10 kafin aka samu matsaya a sabon mafi ƙarancin albashi.”
A cewarsa, ya kamata ne gwamnati ta biya bashin cikon albashin na wata goma, “amma sai na wata shida kawai gwamnatin ta biya. Ke na ma’aikatan suna bin bashin cikon albashi na wata huɗu.
Atiku ya zargi gwamnatin da amfani da ƙarfi wajen “hana furta albarkacin baki maimakon neman matsaya ta hanyar tattaunawa.”
“Mako biyu da suka gabata an kama tare da tsare Andrewa Uche Emelieze saboda ya yi yunƙurin shirya zanga-zangar lumana. Cigaba da tsare ba ƙaramin cin fuska ba ne ga dimokuraɗiyyar Najeriya, har da cin fuska ga dukkan ma’aikatan ƙasar.
“Ya kamata a fahimci cewa ba a isa a doki ma’aikatan Najeriya sannan a hana su kuka ba, ballantana a musu barazana ko a manta da buƙatunsu. Lallai matsain tattalin arzikin da ake ciki a Najeriya gaskiya ne, kuma yunwa na ƙara katutu, wanda hakan ya sa gwamnati matakan gyara ya kamata ta ɗauka, ba daƙile masu magana ba.”