Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu da yin rikon sakainar kashi na yin watsi da batun gaskiya.
Atiku ya ce gwamnatin Tinubu ta yi biris da al’amuran da suka shafi bin ka’ida wajen gudanar da ayyukan gwamnati.
Da yake aikawa a kan X, tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya ce bashin dala biliyan 3.3 na NNPCL da ba a warware ba, shaida ce ga matsalolin cin hanci da rashawa da gwamnatin Tinubu.
A cewar Atiku: “Gwamnatin tarayya mai ci a halin yanzu tana da tarihin rashin kula da al’amuran da suka shafi gaskiya da adalci a harkokin gudanar da gwamnati.
“Bayan nan badakalar biyan bashin dala biliyan 3.3 na NNPCPL da ba a warware ba, inda a yanzu ake sa ran Najeriya za ta biya dala biliyan 12, ya kasance babban misali.
“Dole ne gwamnatin Tinubu ta magance wadannan manyan laifukan cin hanci da rashawa a fili.
“Majalisar kasa, a matsayinta na zababbun wakilan jama’a, wajibi ne a tsarin mulkin kasa ta samar da doka don samar da zaman lafiya, oda, da shugabanci nagari na al’ummarmu, ba tare da hada baki da gurbatattun mutane ba.
“Rashin yin haka da dagewa a cikin musantawa zai tabbatar da hadin kai da gwamnati ke yi a cikin rashin adalci a hukumance.-AA”