Ƙungiyar gwamnonin yankin arewa maso gabashin kasar nan, sun bayyana damuwarsu kan yadda suka ce gwamnatin tarayyar na nuna musu wariya a ɓangren ayyukan ci gaba da gwamnatin tarayya ke yi, musamman titunan mota da layin dogo da za su haɗa yankin da sauran sassan ƙasar.
Gwamnonin – da suka haɗa na jihohin Adamawa da Bauchi da Borno da Gombe da Taraba da kuma Yobe – sun gudanar da taron ƙungiyar ne karo na 10 ranar Juma’a a jihar Bauchi.
Cikin sanarwar bayan taro da gwamnonin suka fitar, sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta dubi yankinsu wajen samar da waɗannan abubuwan more rayuwa.
Gwamnonin sun kuma nuna rashin daɗinsu kan matsalar rashin wutar lantarki da ilahirin yankin arewa maso gabas ya jima yana fama da ita, da kuma yadda kamfanin dakon lantarki na ƙasar TCN ke nuna halin ko’in kula game da batun.
Gwmanonin sun kuma yaba da irin hadin kan da suka bai wa juna wajen ciyar da yankinsu gaba a fannoni daban-daban.