fidelitybank

Tinubu na neman izinin karɓo bashin dala biliyan 21.5

Date:

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya aike wa majalisar dattawa da buƙata inda yake neman izini domin karɓo bashin dala biliyan 21.5 daga ƙasashen waje da kuma naira biliyan 758 daga cikin gida.

Ana sa ran za a yi amfani da kuɗin wajen aiwatar da muhimman ayyuka kamar gyaran hanyoyi da kiwon lafiya da ilimi da samar da ruwan sha da kuma biyan tsoffin ma’aikata haƙƙoƙin fansho da ake bin su a ƙarƙashin tsarin Fansho na Gwamnati

Majalisar ta tura buƙatar zuwa kwamitinta mai kula da lamurran bashi na cikin gida da na waje, wanda ake sa ran zai kawo rahoto cikin makonni biyu.

Haka kuma, Shugaban ya buƙaci a ba shi damar cin bashin ƙarin dala biliyan biyu daga kasuwar cikin gida domin saka jari a wasu sassa masu muhimmanci na tattalin arziƙi wanda shi ma majalisar za ta tura zuwa ga kwamitin basussuka na gida da waje domin nazari.

A baya, Tinubu ya rubuta wa majalisar yana neman amincewa da sabon shirin rancen kuɗi na shekarar 2025 zuwa 2026.

bbc naija news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp