fidelitybank

Tinubu na jimamin Sojojin da Boko Haram ta kashe a Borno

Date:

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya yi alhinin rasuwar dakarun Sojojin da aka kashe a harin da mayaƙan Boko Haram ta kai wani sansanin soji da ke ƙauyen Sabon Gida, cikin ƙaramar hukumar Damboa a jihar Borno.

Cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin ƙasar ta fitar, ta ce Tinubu ya jajanta wa rundunar sojin ƙasar sakamakon mutuwar dakarunta shida a harin.

Haka kuma shugaban ƙasar, ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike domin gano abin da ya haddasa harin, domin ɗaukar matakan hana faruwar makamancinsa a nan gaba”.

A ranar Asabar ne mayaƙan ISWAP suka ƙaddamar da hari da asuba kan sansanin sojin inda suka yi arangama da sojoji, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin ƙasar shida da mayaƙa fiye da 30.

Shugaba Tinubu ya kuma yaba wa sojojin ƙasar bisa jajirewar da suka yi, har ta kai ga sun samu nasarar daƙile harin harin, tare da kashe gomman mayaƙan ƙungiyar.

legit nigeria news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp