Shugaban kasar Guinea-Bissau, Umaro Sissoco Embaló a halin yanzu yana ganawa da shugaba Bola Tinubu.
Tinubu ya tarbi takwaransa na Guinea-Bissau wanda ya zama shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, ECOWAS a gidansa da ke Legas ranar Asabar.
Ba za a iya samun cikakken bayani game da taron ba har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.
A ranar 10 ga watan Fabrairun 2023 ne shugaba Umaro ya ziyarci kasar a lokacin da ya gana da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari gabanin babban zabe.