fidelitybank

Tinubu na ƙwato kuɗaɗen da aka sace a gwamnatocin baya – Sarkin Minna

Date:

Sarkin Minna, Alhaji Umar Farouk Bahago ya ce shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi bakin ƙoƙarinsa wajen ƙwato kuɗaɗen da aka sace a gwamnatocin baya, amma ƴan Najeriya ba su gane ba.

Sarkin ya bayyana hakan a taron wayar da kan ƴan ƙasa a kan tallafin da Gwamnatin Tarayya ke yi a jihohin ƙasar, wanda ofishin Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma ya shirya a Minna na Jihar Neja.

Sarkin wanda Hadinin Minna, Alhaji Maukudi Achaza ya wakilta, ya ce Tinubu na bakin ƙoƙarinsa wajen magance matsalar cin hancin da rashawar da aka yi a baya.

Ya ce tallafin da gwamnatin Tinubu ke yi, yawancin ƴan ƙasar ba su sani ba saboda masu magana da yawun gwamnatin ba sa yaɗa ayyukan yadda ya kamata musamman wajen yin magana da harshen da mutanen ke ji.

“An sace maƙudan kuɗaɗe da dama a gwamnatocin baya, wanda gwamnatin yanzu ke ƙoƙarin ƙwatowa, amma mutane da dama ba su fahimta ba. Sannan tun bayan janye tallafin man fetur, an gudanar da abubuwa da dama domin rage raɗaɗin da ƴan ƙasa suka shiga. Yana da kyau gwamnati ta riƙa wayar da kan mutane a kan shirye-shiryenta a harshen da suke ji,” in ji shi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

leadership news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...
X whatsapp