Kungiyar gwamnonin jam’iyyar Peoples Democratic Party Forum ta godewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, bisa nada tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike a matsayin ministan babban birnin tarayya.
Kungiyar Gwamnonin PDP ta kai ziyarar ban girma ga Ministan babban birnin tarayya a ranar Larabar da ta gabata sakamakon rikicin siyasa da ya barke a gidan gwamnatin jihar Ribas.
Shugaban kungiyar kuma tsohon ministan babban birnin tarayya, Bala Mohammed, wanda ya yi magana bayan taron, ya yaba wa Tinubu kan nada Wike duk da cewa yana cikin jam’iyyar adawa.
A cewarsa, “A cikin hadarin da ake yi mana na zarge-zarge, muna matukar godiya ga shugaban kasa da Nyesom Wike. Haka kuma, ba shi wannan ofishi a babban birnin tarayya Abuja, wanda tamkar jiha ne, duk da kasancewarsa daya daga cikin mu a matsayinsa na dan PDP, ya nuna irin shugabancin da shugaban kasa yake da shi.”