Yayin da ya rage kwanaki 45 a gudanar da zaben shugaban kasa, jam’iyyar Labour Party, LP, dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, ya ce kujerar shugaban kasa ba gado ba ne.
Da ya ke tsokaci kan takwaransa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ya ce, lokaci ne na ‘yan Najeriya da na Kudu maso Gabas su zama shugaban kasa.
Ya yi wannan jawabi ne a jiya yayin gangamin yakin neman zabensa a jihar Delta.
A cewar Obi: “Wani ya ce, lokacin sa ne ya zama shugaban kasa, ina so in gaya muku cewa, shugaban ba wai bi-bi-da-bi ba ne. Idan bi da bi, ya kamata ya zama nawa, amma ba mu yi amfani da bi da bi ba. Lokaci ne na ’yan Najeriya su zama shugaban kasa musamman masu cike da kuzari.”
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce, ‘yan Najeriya su dora masa alhakinsa idan har ya gaza a fannin tsaro da tattalin arziki idan aka zabe shi shugaban kasa.
“Ku kama ni idan muka gaza a fannin tsaro, tattalin arziki. Za mu sake sa kasar ta yi aiki,” inji shi.
Ya kuma yi alkawarin tabbatar da ganin an kawo karshen yajin aikin a fannin ilimi idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.