Sheikh Sidi Aliyu Sise, Daraktan Ilimi na gidauniyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya roki Tinubu da kada ya rantse da ‘yan siyasa azzalumai.
A cewarsa, nadin El-Rufai da tantance shi da Majalisar ta yi rashin adalci ne ga masu haddar Al-Qur’ani da masu karatu.
Ya yi zargin cewa El-rufa’i ya zalunci Almajirai a karkashin shugabancinsa lokacin yana gwamna.
Ya yi kira ga Tinubu da ya tafiyar da mulkin kasar nan da idon basira.
Sheikh Sidi ya roki cewa, “Muna neman a yi mana adalci a sakamakon rashin adalci, tsangwama, tashin hankali, da wahalhalu da almajiranmu da malamanmu da malaman Alkur’ani da dama suka fuskanta, a lokacin da ya kwashe dalibanmu da ba su ji ba ba su gani ba daga gidan Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Kaduna zuwa inda ba a sani ba.”
Ya ce rantsar da El-rufa’i a matsayin minista na nufin Tinubu na goyon bayan zaluncin da aka yi musu a lokacin da El-rufa’i yake gwamna.