Wata gamayyar ƙwararru ƴan Najeriya, ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi taka-tsantsan wajen ɗaukar matakan mayar da jamhuriyar Nijar kan turbar dimokraɗiyya, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa shugaba Mohamed Bazoum.
A wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da gamayyar ta aika wa Shugaba Tinubu, ta ce akwai buƙatar Najeriya ta zamo mai sara tana duban bakin gatari game da matsayarta a kan abin da ke faruwa a Nijar, musamman bisa la’akari da daɗaɗɗiyar dangantaka mai kyau tsakanin ƙasashen biyu, aminan juna.
Shugaban na Najeriya, Bola Tinubu, shi ne ke jagorantar Ƙungiyar Raya Ƙasashen Afirka ta Yamma wato Ecowas da ta bai wa sojoji masu mulki a Nijar wa’adin kwana bakwai don su mayar da mulki hannun hamɓararren shugaban ƙasa Bazoum Mohamed ko kuma ta ɗauki matakin amfani da ƙarfi a kansu.
Gamayyar wadda ta ƙunshi ƙwararru daga ɓangarori daban-daban na rayuwa, ta bi sahun Ecowas da sauran ƙasashen da ƙungiyoyin duniya wajen yin Allah-wadai da juyin mulkin na Nijar, amma ta ce hanyar lumana ta fi dacewa a bi wajen warware matsalar.
Ta jaddada goyon bayanta ga yin amfani da sarakuna da malaman addini da kuma ƙungiyoyi wajen tuntuɓa da neman maslaha tsakanin sojojin da suka ƙwace mulki a Nijar don kaucewa duk wani abu da zai ta’azzara rikici.
Haka kuma, gamayyar ta fargar da Shugaba Tinubu a kan buƙatar inganta hanyar fitar da bayanai game da matakan da ake ɗauka a kan Nijar don kaucewa faɗawa tarkon masu yaɗa labaran bogi kan matsayar Najeriya da ma shugaba Tinubu game da wannan dambarwa