Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya shawarci shugaban kasa Bola Tinubu da ya sauke duk wanda ya nada wanda ya kasa cika aikin sa.
El-Rufai ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Maiduguri a ranar Litinin, inda ya bukaci shugaban kasar da ya kuma duba yiwuwar gyara wasu manufofinsa da ba sa samar da sakamakon da ake bukata.
“Kun nada mutum mukami kuma ba ya aiki yadda ake tsammani, ya kamata ku kasance da tawali’u don gaya masa cewa ina bukatan wanda ya fi ni, je ku yi wani abu daban,” in ji El-Rufai.
El-Rufai ya kuma yi kira da a yi addu’a da goyon bayan ’yan kasa ga gwamnati a yunkurinta na ganin ta dawo da al’amura.
“Abin da ya kamata mu yi a matsayinmu na ’yan kasa shi ne mu yi wa shugabanninmu addu’a don Allah Ya yi musu jagora su gani ko su yi abin da ya dace.
“Domin Allah ya ba su tawali’u su juyar da kansu a lokacin da ya dace kuma su yi abin da ya dace; haka al’umma ke ci gaba,” in ji shi.