fidelitybank

Tinubu ka samar da kudaden da za a gina tituna na siminti – Kungiyar Inyamurai

Date:

Kungiyar koli ta al’adun kabilar Igbo, Ohanaeze Ndigbo, ta yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya samar da kudade na musamman ga ma’aikatar ayyuka karkashin jagorancin Dave Umahi domin gudanar da gyara ababen more rayuwa, gyaran fuska, da gine-ginen siminti da fasaha a yankin kudu maso gabas sauran sassan kasar nan.

Kiran na Ohanaeze ya biyo bayan umarnin Gwamnatin Tarayya na cewa ’yan kwangila su canza daga hanyoyin kwalta zuwa fasahar siminti don shimfida titina a yankin kudu maso gabas da sauran sassan kasar nan.

Kungiyar koli ta Igbo ta yabawa gwamnatin tarayya bisa umarnin da ta bayar, inda ta ce za ta tabbatar da gina hanyoyi masu inganci tare da tsawon shekaru 30.

A cikin wata sanarwa da babban sakataren kungiyar Okechukwu Isiguzoro, Ohanaeze, ya fitar, ya nuna damuwarsa kan cewa ma’aikatar ayyuka ba za ta samu kudaden da ake bukata don aiwatar da wannan umarni ba.

Don haka kungiyar ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi amfani da “Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC) wajen samar da kudade na musamman ga ma’aikatar ayyuka.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Ohanaeze ya ce hakan zai baiwa ma’aikatar damar daidaita ‘yan kwangilar tare da tabbatar da cewa sun samar da ingantattun hanyoyi da tsawon shekaru 30.

“Ya kamata Tinubu ya tabbatar da cewa kudade ba za su hana ‘yan kwangilar tituna na tarayya ba wajen tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun more ingantattun hanyoyi ta hanyar gina manyan titunan gwamnatin tarayya da siminti da fasahar siminti.”

Ohanaeze ya ce ‘yan Najeriya na goyon bayan umarnin ma’aikatar ayyuka na a sake duba kwangilolin ‘yan kwangila domin biyan bukatun ‘yan Najeriya da ke matukar bukatar ingantattun hanyoyi a fadin kasar.

Kungiyar ta ce Tinubu zai ba da fifikon burin ‘yan Najeriya a kodayaushe, musamman a yunkurin samar da ababen more rayuwa wanda ya dace da tsarin FATAN BEGE.

Ohanaeze ya ce, “Kudaden shiga tsakani na musamman na NNPC zai kara wa ma’aikatar ayyuka kwarin gwiwar tabbatar da cewa ‘yan kwangilar hanyoyin tarayya za su bi sabbin ka’idojin yin amfani da fasahar siminti wanda ke da tsada fiye da kwalta kawai hanyar da ke lalacewa bayan damina. ”

naija news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp