Wata kungiya mai bibiyar harkokin kasafin kudi da ake kira BudgIT Nigeria, ta nemi gwamnatin Tinubu ta sake nazarin kudurin kasafin kudin 2024 da Shugaba Bola Tinubu ya gabatarwa majalisa.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta wallafa a shafinta na X wanda a baya ake kira Tuwita, BudgIT Nigeria ta bayyana damuwar cewa bayan cikakken nazari kan abin da kudurin kasafin kudin ya kunsa, ta lura cewa gwamnatin Tinubu ta ci gaba da aiki da tsarin kasafin kudi mai cutarwa daga gwamnatin da ta gabata, da ke dabbaka cin hanci da rashawa da rashin aikin yi da kuma fatara.
Sanarwar ta ce wani muhimmin abu da ta lura da shi, shi ne rashin sanya bayanan kasafin kudi dalla-dalla na wasu hukumomi da ma’aikatun gwamnati a cikin kudurin kasafin kudin.
Ta ce ga misali babu bayanai dalla-dalla na kasafin kudin majalisar dokokin Najeriya da Hukumar raya yankin Neja Delta da hukumar raya yankin Arewa maso Gabas, sannan ba a ga kudurin kasafin kudin hukumomin kasar da dama ba.
Kungiyar ta kuma ce nazarinta ya gano maimaicin ayyukan da aka warewa kudi a cikin kasafin daga ciki akwai kudin aikin gyara gidajen shugaban kasa da na mataimakinsa.
Ta yi ikirarin cewa tun a baya cikin kwarya-kwayan kasafin kudin 2023, an ware naira biliyan takwas don gyara gidajen shugaban kasa da na mataimakinsa a fadar Aso Rock da kuma na Dodon Barrack da ke Lagos, sai dai abin mamaki in ji kungiyar sai aka sake ware naira miliyan 500 don gyaran gidan shugaban kasa na Aso Rock, yayin da aka ware naira biliyan biyar don gyaran gidan Dodon Barrack a kwarya-kwaryan kasafin kudin 2023, sannan kuma aka sake gabatar da kudurin gyara gidajen a kan naira biliyan tara da miliyan 300 a kasafin 2024.