Tsohon shugaban tsagerun Neja Delta, Asari Dokubo, ya yi tsokaci kan yadda shugaba Bola Tinubu ya kori wasu manyan ‘yan Najeriya da ke shugabancin hukumomin gwamnati.
Dokubo dai na mayar da martani ne kan korar Godwin Emefiele a matsayin Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN da Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban riko na Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati ta EFCC.
Da korar Bawa da Emefiele, Dokubo ya ce, Tinubu zai tabbatar da cewa an samu karin wasu.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da wakilin gidan gwamnatin jihar bayan ganawarsa da Tinubu a jiya.
A cewar Dokubo: “Emefiele ya tafi, Bawa ya tafi, don haka wasu kawuna za su yi birgima.
“Wadanda ke tsaye a matsayin masu kawo cikas ga ci gaban kasar nan, Shugaban kasa ba zai yi amfani da su ba.
“Shugaban kasa zai kori duk masu adawa da ci gaban kasar nan, kuma idan ya yi haka za mu samu karfin gwiwar kawar da satar mai.”


