fidelitybank

Tinubu ka kafa ƴan sandan jihohi – Gwamnonin PDP

Date:

Gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP, sun yi kira da a kafa rundunonin ƴansanda na jihohi a karkashin wata doka da zata hana yin katsalandan daga duka matakan gwamnati.

Sun jaddada hakan ne a wurin wani taro da suka yi a ranar Litinin a Abuja.

Taron ya kuma tattauna yanayin da ƙasar ta tsinci kanta game da wahalhulun da mutane ke fuskanta ta fuskar tattalin arziki da kuma tsaro.

Inda suka buƙaci gwamnati da ta ɗauki matakan gaggawa wajen ɓullo da wasu shirye-shirye da za su haɗa da duka ɓangarorin gwamnati don samar da mafita mai ɗorewa.

Gwamnonin na PDP sun kuma sha alwashin ci gaba da taka rawar da ta dace domin samar da tsaro ga al’ummansu, abun da a cewarsa ya sa suka jaddada buƙatar kafa ƴansandan jiha.

Taron ya kuma koka kan karyewar darajar kudin ƙasar wato naira, inda suka nemi hukumomin da abun ya shafa da su ɗauki matakan da suka dace domin magance matsalar.

Sai dai jihar Zamfara da ta Filato na daga cikin jihohin da jam’iyyar ta PDP ke mulki, kuma suke kan gaba wajen fuskantar matsalar tsaro da tashe-tashen hankula a tsawon shekaru.

Lamarin da ya yi sanadiyyar asarar dubban rayuka da ta dukiyoyi.

spw

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp