Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar LP, Peter Obi, ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya fito ya fayyace gaskiya game da rayuwarsa.
Obi ya bayyana haka ne a wata ganawa da manema labaru yau Laraba a birnin Abuja.
A lokacin ganawar, Peter Obi ya ce: “Ina kira gare shi (Tinubu) ba tare da ɓata lokaci ba ya yi abu mai sauƙi, ya bayyana wa al’ummar ƙasar da yake mulka ko shi wane ne domin kawar da duk wani shakku.”
“Ya kamata ya sanar da duniya asalin sunansa, da ƙasarsa da inda aka haife shi da iyayensa da makarantun sakandare da firamaren da ya halarta da jam’iar da ya halarta da kuma takardun shaidar kammala karatun.”
Hakan na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan da ɗan takarar shugaban Najeriya na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a lokacin wani taron manema labaru ya yi zargin cewa Tinubu ya gabatar da takardun bogi domin tsayawa takarar shugaban ƙasa.
Batun asalin Bola Tinubu da karatunsa lamari ne da ke janyo ce-ce-ku-ce tun lokacin da shugaban na Najeriya ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa.
Tuni dai jami’ar jihar Chicago da ke Amurka, wadda Tinubu ya bayyana cewa ya halarta ta saki bayanai da suka tabbatar da cewa ya halarci makarantar, inda ya samu shaidar kammala karatun digiri.
Sai dai har yanzu ƴan takarar shugaban ƙasa na manyan jam’iyyun adawa biyu a zaɓen na watan Fabarairun 2023 na nuna shakku tare da cewa suna da shaidun da ke nuna cewa Tinubu ya yi amfani da takardun bogi domin samun damar yin takara