An shawarci zababben shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu kan yadda za a nada gwamnan babban bankin Najeriya CBN.
Deji Adeyanju, wani mai fafutukar zamantakewa da siyasa, ya ce, ya kamata gwamnatin Tinubu mai zuwa ta nada wani mashahurin masanin tattalin arziki a matsayin gwamnan CBN na gaba.
Adeyanju ya ce kamata ya yi gwamnan babban bankin na CBN ya samu gogewar aiki da cibiyoyin hada-hadar kudi irin su asusun ba da lamuni na duniya IMF, da bankin duniya.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Adeyanju ya bukaci gwamnatin Tinubu da ta daina nada ma’aikatan banki a matsayin gwamnonin CBN.
A cewar Adeyanju: “Dole ne FG ta daina nada ma’aikatan banki a matsayin Gwamnan CBN ba su san komai ba game da tattalin arziki.
“WaÉ—annan Æ´an kasuwa ne kawai. Masanin tattalin arziki da ya shahara da gogewa wajen aiki da cibiyoyin hada-hadar kudi da sassan duniya kamar IMF, Bankin Duniya da dai sauransu, ya kamata ya zama Gwmnatin CBN na gaba.”
An nada Emefiele ne a ranar 4 ga watan Yuni, 2014 kuma ana sa ran wa’adinsa na biyu zai kare a shekarar 2024.
A lokacin yakin neman zabe, CBN ya bullo da wata manufa ta kudi wacce ta shafi ‘yan Najeriya kuma ta yi kusan bata nasarar Tinubu.