fidelitybank

Tinubu ka dakatar da harajin VAT – Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa

Date:

Majalisar tattalin arzikin ƙasa NEC, ta shawarci shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya janye ƙudurin yi wa harajin VAT garambawul da ya aika majalisar dokokin ƙasa domin a samu isasshen lokacin da za a tattauna tare da fahimtar juna game da abin da ake nufi gyara VAT ɗin.

Tun da farko gwamnonin Arewa da sarakunan yankin sun yi zama na musamman a Kaduna tare da wasu masu ruwa da tsaki a yankin, inda suka yi fatali da ƙudirin na shugaban ƙasa.

Majalisar ta bayyana hakan ne bayan zamanta na 145 a ƙarƙashin mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima a Abuja.

Majalisar ta ɗauki wannan matakin ne bayan shugaban kwamitin shugaban ƙasa na musamman kan tsare-tsare da yi wa haraji garambawul, Mista Taiwo Oyedele ya gabatar da jawabi game da tsare-tsaren da suke yi, inda majalisar ta ce akwai buƙatar a samu ƙarin lokaci domin tattaunawa tare da fahimtar juna.

Haka kuma Kashim Shettima ya ce za su ɗauki matakai da suka dace domin tabbatar da ba a sake samun irin katsewar lantarkin da aka fuskanta ba a kwanankin baya.

dailypost news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Tinubu zai magantu a kan ranar Dimokradiyya

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai yi jawabi ga...

A shirye nake na mutu don nasarar APC a 2027 – Orji Kalu

Sanatan Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana...

Bayan hutun Sallah Tinubu zai koma Abuja

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu na kan hanyarsa ta komawa...

Mutane 570 aka kashe a Najeriya cikin watan Afrilu – Rahoto

Hukumar kare haƙƙin ɗan'adam a Najeriya ta ce, adadin...

PDP ba za ta mutu ba duk da rikicin cikin gida – Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ce...

Sojoji sun kashe riƙaƙen ɗan bindiga Guddel a Kaduna

Sojoji sun yi nasarar kawar da fitaccen shugaban ‘yan...

Fadar shugaban ƙasa ta yi kakkausar gargaɗi a kan Ndume

Fadar shugaban kasa ta yi kakkausar gargadi ga dan...

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...
X whatsapp