fidelitybank

Tinubu ka bullo da hanyar magance wahalhalun ‘yan Najeriya – Tinubu

Date:

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce dole ne gwamnati mai ci ta ɓullo da hanyar magance wahalhalun da ƴan Najeriya ke ciki a wannan lokaci.

Atiku ya bayyana haka ne a sakonsa na barka da sabuwar shekara ga ƴan Najeriya.

Ya ce dole gwamnati ta nuna wa ƴan ƙasa alkibla ko kuma inda manufofinta suka dosa ba wai barinsu a cikin duhu ba.

“Da gwamnati ta yi dabara wajen tsara manufofinta da ba mu shiga irin wannan kangi da muke ciki ba. Iyalai da kuma masana’antu da yawa na cikin wane hali a yanzu,” in ji Atiku.

Ya ce ya zama tilas a tashi domin fuskantar batun hauhawar farashin kayayyaki, taɓarɓarewar tattalin arziki da kuma rashin tsaro a sabuwar shekara da nufin magance su.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce shekara ta 2023 na cike da kalubale masu tarin yawa, sai dai ya kamata a ɗauki darasi domin fuskantar gaba.

“Idan muna son fita daga wannan kunci da muke ciki, dole ne mu yi tunani mai kyau da kuma samar da tsare-tsare na ƙasa waɗanda za su sa talakawan Najeriya su zama ginshikin ci gaban mu,” in ji Atiku.

Wazirin na Adamawa ya taya dukkan ƴan Najeriya murnar sabuwar shekara tare da yin kira ga kowa da ya tashi haikan don ganin iyalai da sana’o’in sun kasance cikin yanayi mai kyau.

spw news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp